(ABNA24.com) Alkalumman da kamfanin dilancin labaren AFP, ya fitar sun nuna cewa ya zuwa yammacin ranar Lahadi, cutar ta harbi mutum sama da miliyan 8,890,310 a kasashe da yankuna 196 na duniya.
Hakazalika a cewar alkalumman akwai mutum kimanin miliyan 4,139,100 da suka warke daga cutar a duniya baki daya.
Saidai bayanin ya ce wadanan alkalumman kaso ne kadan ne daga cikin ainahin yawan mutanen da suka harbu da cutar a zahiri, saboda a wasu kasashen duniya mutanen da yanayinsu ya tabarbare ne ake wa wajin cutar, Sannan kasashe matalauta kayan gwajin da suke da su kayadadu ne.
Kasashen dake sahun gaba wajen yawan wadanda cutar ta kashe a duniya, sun hada da Amurka, Brazil, Biritaniya, Italiya.
/129
22 Yuni 2020 - 09:50
Lambar labari: 1049012
Adadin mutanen da cutar Korona, ta kashe a duniya ya kai akalla 465,300 a duniya, tun bayan bullarta a watan Disamban bara a kasar China.